Niger: Mata na sana'ar karfi don samun abin rufin asiri

Asalin hoton, Getty Images
Matan na sana'o'in ne dan tallafawa mazajensu
A Jihar Damagaram na jamhuriyyar Nijar mata na ci gaba da shiga ayyukan karfi domin neman abinda zasu ciyar da 'ya'yansu.
Daya daga cikin irin wadannan ayyukan karfi da suke yi shi ne na fasa dutse domin sayar da tsakuwa ga masu ayyukan gine-gine.
Wakiliyarmu Tchima Illa Issoufou ta ziyarci wani wurin da mata ke aikin fasa dutsen a wajen birnin Damagaram, inda ta gansu sun dage su na wannan aiki.
Wasu daga cikin matan dai sun zo aikin ne tare da 'ya'yansu mata, a cewarsu idan yaro baya zuwa makaranta gara a sama masa sana'ar yi saboda idan ya fita ba a san inda suke zuwa ba ko abokan da suke mu'amala da su.
Mata a Jamhuriyar Nijar na kokarin neman na kan su dan rage radadin talauci.