Israel: Zamu ginawa Yahudawa dubban gidaje

Benyamin Netanyahu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ba wannan ne karon farko da Isra'ila ke gini a matsugunin Falasdinawa ba a gabar kogin Jordan

Fadar White House ta sanar da cewa gwamnatiu shugaba Trump ba ta dauki matsaya a hukumance kan mamayar matsugunan Palasdinawa da Isaraela ta yi ba, sai dai sake gina wasu matsugunan da fadada yakin da Israela za ta yi iko da zai kawo nakasu a kokarin zaman lafiyar da ake son ya tabbata a yankin.

Wannan sanarwar ta zo ne sa'a guda bayan Firai ministan israela Benyamin Netanyahu ya yi alkawarin gwamnatinsa za ta bada izinin sake gina wasu matsugunan a yankin Plasdinawa bayan an dakatar da ginin yankin Amona.

Sai dai Netanyahun bai yi bayanin lokaci ko wurin da za a yi ginin ba, amma tuni ya samar da kwamitin da zai duba wurin da ya kamata a yi ginin da kuma lokaci.

Ya kara da cewa za a ginawa Yahudawan gidaje 6000, dan wanke takaicin da su ke ciki na raba su da muhallansu da dukiyoyin sun da aka yi.