Jirgin Lufthansa ba zai koma filin jirgin Kaduna ba

Jirgin saman Lufthansa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kamfanin bai yi karin bayani a kan dalilin da ya sa ya dauki wannan matakin ba

A baya-bayan nan ne gwamnatin Najeriya ta ce za ta dakatar da tashin jirage daga Abuja babban birnin kasar saboda wasu gyare-gyare da za a yi a watan gobe.

Wani mai magana da yawun Lufthansa ya ce jiragensu ba za su tashi daga Kaduna ba a lokacin da za a gudanar da gyare-gyaren filin jiragen saman Abuja.

Gwamnatin Najeriya ta ce kamfanonin jiregan sama za su yi amfani da filin jirgin Kaduna da ke arewacin Najeriya a yayin da ake aikin gyaran makonnin 6 daga ranar 8 ga watan Maris din shekarar 2017.

"Ba za mu tashi daga Kaduna ba a lokacin da za a rufe filin jiragen saman Abuja na tsawon makonnin 6, kamar yadda mai magana da yawun jirigin ya bayyana wa Reuters ta wayar tarho.

Sai dai bai yi karin bayani a kan dalilin da ya sa kamfanin ya dauki wannan mataki ba.

Titunan filin jiragen saman sun yi matukar lalacewa inda ta kai ga wasu jiragen kasashen waje ma suke kin tashi, har ma wasu jiragen sun yi korafin titunan na lalata musu jiragensu.