Zanga-zanga: 'Yan sanda sun yi barazanar kama 2face

2face Idibia

Asalin hoton, 2face twitter handle

Bayanan hoto,

2face ya ce zanga-zangar na nufin jawo hankalin gwamnati da ta dauki mataki a kan yadda tattalin arzikin Najeriya ke ci gaba da tabarbarewa

2face Idibia ya ce ya shirya zanga-zangar ne saboda ya jawo hankalin gwamnatin kasar a kan yadda tattalin arzikinta ke ci gaba da tabarbarewa da kuma tsadar kayayyaki.

Mawakin ya bukaci gwamnati ta yi wa 'yan Najeriya bayani cikin gaggawa a kan yadda tattalin arzikin kasar ya sauya alkibla.

Baya ga wadanda za su yi zanga-zangar a shafin Twitter, za a kuma gudanar da zanga-zangar zahiri a biranen Lagos da Abuja.

Shugaban 'yan sandan jihar Lagos, Fatai Owoseni, ya ce ba a shaidawa jami'an tsaro cewa za a yi zanga-zangar ba.

Hukumar ta kuma ce ba za ta bari a gudanar ba saboda wasu bayannan sirri sun nuna cewa, "Wasu bata gari na da niyyar mamaye tare da cuzgunawa jama'a da kuma kai hari kan mutane."

Tuni dai batun zanga-zangar ya mamaye shafukan sada zumunta da muhawarar kasar, inda wasu ke goyon bayan aniyar mawakin wasu kuma suna tir da hakan.