MDD ta yi gargadin bullar tsutsotsi a Afirka

Tsutsotsin gona
Bayanan hoto,

Bazuwan tsutsotsin na iya lalata daukacin gona

Hukamar samar da abinci da ta gona ta majalisar dinkin duniya ta yi gargadin cewa mai yiwuwa tsutsotsin da ke yi wa shuka ta'adi sun bazu zuwa kasashen kudancin Afirka guda 6.

Zimbabwe dai ta tabbatar da akwai wadannan tsutsotsin a cikin kasar.

Ana kuma zargin akwai su a kasashen Malawai da Mozambique da Namibia da Afirka ta kudu da kuma Zambia.

Majalisar ta ce bullar tsutsotsin abin damuwa ne, saboda yankin farin da yankin ya yi fama da shi a bara.

Lamarin yashafi shuka sannan kuma yasa miliyoyin mutane cikin bukatar tallafin abinci.