Amurka ta gargadi Korea ta Arewa kan amfani da nukiliya

Korea ta Arewa

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Mista Mattis yana hira da takwaransa na Korea ta Kudu, Han Min-koo

Sakataren Tsaro na Amurka James Mattis, ya ce daga yanzu a shirye kasarsa take ta mayar da martani mai tasiri kan duk wani amfani da makaman nukiliya da Korea ta Arewa za ta yi.

Mista Mattis ya bayar da wannan sanarwa ne a Korea ta Kudu, inda yake jaddada goyon bayan da Amurka za ta ba ta, kafin ya tafi Tokyo.

Ya kuma jaddada cewa Amurka na tsare-tsaren yadda za ta tura tsarin kariya daga makami mai linzami a Korea ta Kudu nan gaba a cikin shekarar nan ta 2017.

Gwaje-gwajen makami mai linzami da Korea ta Arewa ke ci gaba da yi da kuma wasu tsauraran kalamanta suna kara tunzura kasashen yankin da sanya su fushi.

Amurka tana da bubban sojoji a Korea ta Kudu da Japan, a bangaren wata yarjejeniyar tsaro bayan yaki.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Sojojin Korea ta Kuda da Amurka su kan yi horo tare

A kalla Amurka na da sojoji 28,500 a kasar, wadanda Seoul ke biyansu dala milliyan 900 ko wacce shekara.

Shugaba Donald Trump ya ce yana son Korea ta Kudu da Japan su kara yawan kudaden da suke biyan sojojin domin Amurka ta ci gaba da zama a kasar don kare ta daga barazanar Korea ta Arewa.

Korea ta Arewa ta gudanar da gwaje-gwaje makaman nukiliya biyar a shekarar da ta wuce, da nufin kai harin nukiliya a Amurka, duk da cewa masana ba su tabbatar da ci gaban fasahar kasar ba.

A 'yan makonnin baya-bayan nan ta sake tabbatar da cewa tana da wani sabon makami mai linzami da ka iya kai wa Amurka, wanda a shirye take ta gwada shi.