Masu cutar sankara na fama da wahalhalu a Nigeria

cancer

Asalin hoton, Getty Images

Cutar sankara ko cancer da turanci na daya daga cikin cututtukan da ke adabar al'umma a wannan zamani, kuma cuta ce da take da matukar wuyar sha'ani.

Cutar tana lakume makudan kudade a wajen magance ta sannan kuma tana halaka dubun dubatar mutane a Najeriya dama duniya baki daya.

Cutar ta sankara tana da nau'o'i daban-daban, akwai ta wuyan mahaifa wato Cervical cancer, akwai sankarar mama, da mai kama hanta, da ta huhu, da ta mafitsara wadda maza suka fi fama da ita, da ta kwakwalwa da ta hanji da ta fata da ta jini da dai sauran su.

A Najeriya dai an fi samun cancer ta mahaifa da ta mama ga mata, da kuma ta mafitsara ga maza.

Kuma a yanzu haka duk da cewa babu wani kididdigaggen adadi a hukamance, ana kiyasin cewa a Najeriya masu fama da wannan cutar sun kai dubban daruruwan mutane. Sai dai mafi yawansu ba su cika son zuwa asibiti ba, don a ganinsu ba ciwon asibiti ba ne.

Me ke jawo cancer?

Masana dai sun ce babu wani takamaiman abu da za a ce shi ke jawo cancer, amma akwai abubuwan da ke sanadinta.

"Yawan shekaru na daya daga cikin abin da ke jawo cancer, da kuma yawan kiba, da yawan zubar da ciki sai kuma yawan haihuwa ba hutawa a tsakani wanda ke iya kawo cancer ta mahaifa", inji Dakta Bello Abubakar, babban likita da ya kware a bangaren magance cancer a babban asibitin kasa da ke Abuja.

Haka kuma bincike ya nuna cewa Turawa sun fi bakaken fata hadarin kamuwa da cutar. Kaza lika mace daya cikin takwas ke kamuwa da cancer ta mama (nono).

Kalubale a harkar a lafiya

Cutar cancer cuta ce da take bukatar ingantattun na'urori na zamani don maganceta, da kuma magunguna. Sai dai a iya cewa a Najeriya ana fama da matsalar rashin kayan aikin.

Dakta Bello Abubakar ya kuma ce,"Watanni biyu da suka gabata babu na'urar da ake amfani da ita wajen magance sankara ko guda daya da take aiki a Najeriya baki daya.

Zuwa ranar 31 ga watan Janairu kuwa, na'urorin da aka samu damar gyara su suka dawo bakin aiki su ne wadanda suke asibitin koyarwa na jami'ar Lagos LUTH, da na jami'ar Ahmadu Bello Zaria ABUTH da na jami'ar Usman Dandofio Sokoto.

Amma duk da haka cikin na'urorin ba wacce ta ke ta zamani ce mai inganci.

A ziyarar da BBC ta kai babban asibitin kasa, National Hospital Abuja, ta samu babu wata na'ura da ke aikin kona cutar sankara a yanzu haka.

Dakta Abubuakar ya shaida wa BBC cewa, "Kimanin wata shida kenan ba a aikin kona cutar wanda yana da muhimmanci kwarai wajen maganceta."

Sai dai kuma Dakta Abubakar ya ce gwamnati ta kawo wasu sabbin na'urorin na zamani da za su maye gurbin tsoffin, sai dai ba a fara aiki da su ba.

Wannan dalili na rashin ingantaccen tsari a harkar magance sankara ne yasa masu hali kan bar kasar don zuwa kasashen waje neman magani.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masu hali kan fita kasashen waje don neman magani

Da yawansu kan je kasashe irin su Indiya da Hadaddiyar Daular Larabawa da Masar har da ma Ghana.

Haka kuma darakta kan sha'anin sankara a ma'aikatar lafiya ta tarayya Dakta Ramatu, ta ce wasu daga cikin manyan matsalolin da ake fuskanta kuma sun hada da rashin injiniyoyi da suka san harkar gyaran na'urorin da kuma duhun kan da mutane ke fama da shi a kan ciwon.

"Da yawa sai mutane su ki zuwa asibiti saboda a zatonsu ba ciwon asibiti ba ne, kuma zahiri ba haka maganar take ba." Inji Dakta Ramatu.

Mafita

Sai dai a cewar Dakta Ramatu, gwamnati ta dukafa wajen shawo kan wadannan matsaloli, inda ake shirya wayar da kai ta hanyoyi daban-daban, ta yadda za a gamsar da mutane cewa zuwa asibiti da wuri yana sa a iya saurin shawo kan cutar.

Kazalika ta kuma ce ana hobbasa don ganin an samu kwararrun injiniyoyi da za su rika gyara na'urorin akai-akai.

'Majinyata na shan ukuba'

Sai dai matsalar ba a wajen rashin kayan aiki kawai ta tsaya ba. Don kuwa a hirar da BBC ta yi da wasu masu fama da cutar, sun ce babbar matsalarsu ita ce 'tsadar magunguna' wadanda sun fi karfin aljihunsu.

Dakta Abubakar ya ce, "Muna ganin irin wahalhalun da marasa lafiyar nan ke fuskanta wajen sayen magunguna, akwai allurar da ake so masu cancer ta mama su rika amfani da ita duk mako, kuma duk ta mako daya tana kai wa naira dubu 800."

Ya kara da cewa, "A sakamakon haka sai ka ga idan sun tafi ba sa kara dawowa asibiti sai su koma neman maganin gida, in ba a yi sa'a ba lamari sai ya tabarbare."

Wata mara lafiya ta shaida wa BBC cewa, "Ba mu da kudin sayen magani don yayi tsada. Muna rokon gwamnati da ta taimaka mana ta kawo mana agaji, ta sassauta mana yadda za mu iya sayen maganin."

A cewar Dakta Abubakar, kasashe da dama suna tallafawa al'ummominsu wajen basu magungunan kyauta duk kuwa da tsadarsu.

"Haka ya kamata gwamnatin Najeriya ta taimaka ta yi wa masu fama da cutar nan, don kuwa ba karamin jin jiki da na aljihu suke yi ba." Inji Dakta Abubakar

Shin ko ana warkewa daga cutar sankara?

Dakta Abubakar ya ce, "Kwarai da gaske ana warkewa, akwai marasa lafiya da na duba da dama kuma mun gode Allah sun samu lafiya sosai."

Yanzu haka akwai riga-kafi da ake yi don kaucewa kamuwa da wasu fannonin cutar cancer kamar ta mahaifa, inda ake yi wa yara mata daga shekara bakwai zuwa 15.

Matakan magance cancer

Akwai matakai uku da ake bi don magance wannan cuta ta cancer da suka hada da bayar da magani na hadiya ko allura, da tiyata da kuma kona wajen tsiron cutar.

Amma duk hanyoyi ukun suna yi wa mutane da dama wahala saboda rashin walwalar aljihu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana yawan wayar wa da mutane kai a kan cutar cancer

Jinyar masu cutar

Ko ma'aikatan jinya ma sun koka kan cewa babu jinyar da ta fi ta cancer cin rai da wahala.

Wata ma'aikaciyar jinya ta shaida wa BBC cewa, "Abin da wahala sosai don kuwa wani lokaci wari sosai ciwon nasu yake yi, kuma mu ne masu wankewa."

"Amma abin takaicin shi ne babu wani alawus na musamman da ake ba mu kamar yada ake wa takwarorinmu a kasashen da suka ci gaba, kai har da ma makwabtan kasashe.

Don haka muna rokon gwamnati da ta taimaka wa masu jinyar, mu ma kuma a rika kyautata mana don mu samu kwarin gwiwar ci gaba da aikinmu sosai."

Yanzu dai a iya cewa ya rage wa gwamnati ta ji koken masu fama da cutar da kuma korafin ma'aikatan lafiya don bayar da agaji.