Dusar kankara ta hallaka mutane takwas a Afghanistan

Tsaunukan Afghanistan da kankara ta mamaye
Bayanan hoto,

Mazauna yankunan da lamarin ya shafa sun ce wasu gidajen sai an sassabe kankarar kafin a samu shiga ciki

Dusar kankara mai tarin yawa da ta sauka a arewa maso gabashin kasar Afghanistan ta hallaka akalla mutane goma.

Jami'ai yankin na fargabar ta yi wu wasu mutanen sun makale a cikin kankarar, a yankin Badakhshan saboda yadda kankarar ke zuba a wurin.

Kankarar dai ta mamaye gidaje da tituna har ma da motocin da ke aje a kofar gidaje, a yankin na Badakhshan sannan wasu iyalai su goma sha takwas sun rasu sakamakon mamaye gidansu da kankarar ta yi.

Haka kuma kankara da ke zuba a sauran yankunan Afghanistan ciki kuwa har da gundumar Bamiyan da Balkhab da ke arewacin kasar sun sanya harkokin sufuri tsayawa cak.

A gundumar Sari Paul kuwa, masu aikin ceto sun kubutar da mutane kusan saba'in da suka makale a cikin wani gini da shi ma kankarar ta mamaye.