Kotu ta yi watsi da bukatar Trump kan hana musulmai shiga Amurka

Donald Trump Hakkin mallakar hoto AFP/Getty Image
Image caption Trump bai bada wata shaidar da ke kare ikirarin na shi ba

Wata kotun tarayya a Amurka ta yi watsi da bukatar shugaban kasar Donald Trump da ya shigar gaban kotun wajen neman sake hana wasu musulmai shiga kasar, wadda wani alkali ya ce haramtacciya ce, a ranar Juma'a.

Alkalin dai ya ce hana wasu musulmai shiga Amurka haramtaccen al'amari ne, a inda ya yi watsi da hanin na mista Trump.

Daga nan kuma mista Trump ya shigar da kara yana neman a yi watsi da hukuncin da wancan alkalin ya yi, a inda ita ma wannan kotun ta ce hana musulmai shiga Amurka ba shi da hurumi a kundin dokar kasar.

Hakan dai yana nufin yanzu dole a tsagaita dokar hana musulman shiga Amurkar har sai bayan an gama shari'a.

Kotun dai ta ba wa Fadar White House har zuwa ranar Alhamis da ta gabatar da kwararan shaidu kan hana musulman shiga Amurkar.

Da man dai lauyoyin kasar sun ce hanin da aka yi wa wasu musulamai daga kasashe bakwai shiga Amurka, ba shi da tushe a tsarin mulkin kasar.

Sai dai kuma sashen shari'ar kasar ya ce an aiwatar da dokar ne bisa dogaro da dalilan tsaro.

Sashen ya kuma ce shugaban kasa yana da iko kan masu shigi da fice a kasarsa.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dan wasan kokawar Amurkar zai yi wasa a Iran, bayan ta dan yaye wasu matakan da ta dauka kan Amurka.

Iran wadda daya daga cikin kasashe bakwan da aka hana 'yan kasarsu shiga Amurka, ta ce za ta kyale dan wasan kokawar Amurkar ya shiga kasar domin taka wasa, a gasar wasan kokawa da Iran din za ta karbi bakunci nan gaba a cikin wannan watan.

A baya dai Iran din ta hana 'yan wasan kokawar na Amurka bisar shiga kasar, a wani mataki na martani ga dokar hana wasu musulmi shiga Amurkar.

Hukuncin da aka yanke na ranar Juma'a ya ba wa masu rike da bisa wadanda kuma ke tsare a filayen jirgi suna ta faman rige-rige wajen samun jirgi zuwa Amurka.

Tuni dai ma'aikatar cikin gidan Amurka ta fara ba wa mutane bisa wadanda a baya aka hana kuma an umarci jami'an tsaron kasar da ka da su sake kange mutane.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hana musulmai shiga Amurka ya janyo zanga-zanga a fadin duniya

Su ma jami'an Hana Fasa Kwauri sun fada wa kamfanin jirage cewa za su dawo da jigilar mutanen da aka haramtawa shiga Amurkar.

Kuma kamfanonin jirgi kamar Qatar Airways da Air France da Etihad Airways da Lufthansa da dai sauransu duk su yi maraba da wannan sabuwar doka ta cigaba da jigilar mutanen da a baya aka haramta musu daukar su.

Shi dai wannan hani da shugaba Trump ya fito da shi ya janyo hargitsi a filayen jirgin Amurka da ma na wasu kasashen ketare.

Hanin dai wanda ya kunshi dakatar da bayar da biza na kwana 90 ga mutane daga kasashen musulmi guda bakwai da suka hada da Iraq da Syria da Iran da Libya da Somalia da Sudan da kuma Yemen.

Har wa yau, hanin ya soke shirin Karbar 'Yan gudun Hijra na Amurka har na kwanaki 120 sannan kuma ya haramtawa 'yan gudun hijrar Syria shiga kasar kwata-kwata.

Al'amarin dai ya janyo zanga-zanga a birane a Amurka da ma fadin duniya.