Alƙalin wasan zari-ruga Nigel Owens na son a fiɗiye shi

Nigel Owens

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

A shekarar 2007 ne Nigel Owens ya bayyana cewa shi dan luwadi ne

Alkalin wasan zari-ruga na duniya Nigel Owens ya ce ya je wurin likitansa inda ya nemi a yi amfani da guba wajen dandake shi bayan ya fahimci cewa shi dan luwadi ne.

Ya ce matsin lambar da ya fuskanta a lokacin da ya hura wasan zari-ruga na duniya na shekarar 2015 bata kai ko kusa da matsain lambar da ya fuskanta wajen amicewa shi dan luwadi ne ba.

Alkalin wasan dan yankin Wales yana fama da cutar jarabar cin abinmci da yawan gudawa kuma ya taba yunkurin kashe kansa saboda mutane sun kaurace masa bayan ya ce shi dan luwadi ne.

Owens, wanda shi ne babban jami'in kwallon zari-ruga na farko da ya bayyana cewa shi dan luwadi ne, ya fito fili ya bayyana haka ne a shekarar 2007.

Ya shaida wa shirin Desert Island Discs na BBC Radio 4 cewa: "Hura wasan zari-ruga na duniya tsakanin Australia da New Zealand a gaban mutum 85,000 sannan miliyoyin mutane na kallo a gida, haka kuma kowa na sa ido kan abin da kake yi, bai kai matsin lambar da na fuskanta ta kasancewa ta dan luwadi ba."

Owens, mai shekara 45, ya bayyana cewa tun yana da shekara 34 ne ya gaya wa mahaifiyarsa Mair cewa shi dan luwadi ne.

Ya kara da cewa duk da cewa mahaifinsa Geraint bai gamsu da bayaninsa na zama dan luwadi ba, "amma kaunar da muke yi wa juna ba ta sauya ba."