Manchester United ta doke Leicester City da ci 3-0

Zlatan Ibrahimovic

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

A shekara 35 da kwana 125, Zlatan Ibrahimovic ne dan wasa mafi tsufa da ya zura kwallo 15 a kakar wasan Premier daya

Saura maki daya kungiyar Leicester City da ke kare kambunta a gasar Premier ta fadi daga gasar bayan Manchester United ta doke ta da ci 3-0.

United, wacce ta kai ziyara gidan Leicester, ta zura kwallo biyu a cikin minti biyu.

Henrikh Mkhitaryan ne ya zura kwallon farko bayan ya caje Kasper Schmeichel.

Daga nan kuma Zlatan Ibrahimovic ya zura kwallo ta biyu, kuma kwallonsa ta 15 a kakar wasan Premier ta bana.

Juan Mata ne ya zura kwallo ta uku.

'Yan wasan Leicester ba su tabuka abin a-zo-a-gani ba, domin kuwa sau daya suka kai gagarumin hari ta hannun Wilfred Ndidi.

Har yanzu dai Manchester United na fafutikar ganin ta shiga sahun kungiyoyi hudu na farko.

Amma har yanzu a mataki na shida suke, inda suke bayan Liverpool da maki daya, sannan kuma suke bayan Arsenal, wacce take ta hudu, da maki biyu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Leicester na dab da fita daga Premier