Cameroon ta lashe kofin Afirka

Dan wasan Kamaru

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Wannan shi ne karo na biyar da take daukar kofin

Kasar Kamaru ta lashe gasar cin kofin kwallon kafar nahiyar Afirka a karo na biyar bayan ta doke Masar da ci 2-1.

Vincent Aboubakar, wanda aka sako daga baya ne ya zura kwallon da ta ba su nasara minti biyu kafin a tashi daga wasan.

Tun da farko sai da dan wasan Kamaru Nicolas Nkoulou ya farke kwallon da Masar ta ci su, abin da ya bai wa 'yan wasan kwarin gwiwa.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

'Yan wasan Kamaru sun yi ba-zata

Dan wasan Masar Mohamed Elneny ya soma zura kwallo a miniti 22 da fara wasa.