Trump ya bukaci a sanya ido sosai kan iyakar Amurka

Donald Trump

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Donald Trump ya ce yana cike da fatan ganin ya yi nasara a kan karar

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya shaida wa jami'an kula da kan iyakar kasar su duba mutanen da ke shiga kasar "cikin tsanaki", a daidai lokacin da wasu kotuna suka dakatar da hanin da ya yi wa Musulmi na shiga kasar.

Ya ce kotunan sun "Sanya aikin da nake yi yana zama mai matukar wahala", kuma ya kamata a dora musu alhaki idan wani abu ya faru."

A ranar Asabar ne wasu kotunan daukaka kara suka yi watsi da bukatar da gwamnatin Trump ta mika musu ta hana 'yan gudun hijira da Musulmi shiga kasar bayan wasu kotuna sun soke shirin.

A ranar Juama'a ne wata babbar kotun tarayya ta dakatar da Trump daga aniyarsa ta haramtawa Musulmi daga kasashe bakwai shiga Amurka.

Matakin da kotunan suka dauka na nufin yanzu ba za a yi biyayya ga umarnin Mista Trump ba, kuma duk 'yan daya daga cikin kasashen Irak da Syria da Iran da Libya da Somaliya da Sudan da kuma Yemen din da ke da takardar izinin shiga Amurka, zai samu damar shiga har sai an saurari karar da shugaban ya shigar.

An bai wa fadar White House da kuma jihohin Amurka biyu da ke adawa da hana Musulmi shiga kasar zuwa ranar Litinin domin su gabatar da karin hujjojinsu kan bukatar da suka shigar.

Caccaka

A ranar Lahadi, Mista Trump ya zafafa sukar da yake yi wa alkalin kotun Seattle James Robart, wanda ya hana shi aiwatar da shirin nasa da kuma ma'aiakatar shari'ar Amurka.

A jerin sakonnin da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Mista Trump ya ce, "Na bayar da umarni ga sakataren tsaron cikin gida ya rika caje duk mutumin da zai shigo kasar nan cikin tsanaki".

A cewarsa, "Matakin da alkalin ya dauka na jefa kasar nan cikin hadari yana ba ni mamaki. Idan har wani abu ya faru ya kamata a tuhumi alkalin da kuma kotuna."

Tun da farko dai, Mista Trump ya bayyana matakin da alkali Robart ya dauka a matsayin "abin ban dariya".