Ana zanga-zanga kan 'matsin tattalin arziki' a Nigeria

Protest Lagos
Bayanan hoto,

Da fari tsirarun mutane ne suka fara taruwa a filin wasa da ke Lagos

Daruruwan mutane sun fara hallara a wasu manyan biranen Najeriya don gudanar da zanga-zanga kan matsin tattalin arzikin da kasar ta samu kanta a ciki da kuma hauhawar farashin kayayyaki.

Tun da safiyar Litinin ne dai mutane suka fara taruwa a filin wasa na birnin Lagos, wurin da tuni aka baza jami'an 'yan sanda.

Wakilin BBC ya ce, "Da fari dai jami'an 'yan sandan da aka zuba sun fi masu zanga-zangar yawa, amma daga bisani mutane sun karu har yawansu ya kai daruruwa."

Mutane suna dauke da kwalaye da aka yi rubuce-rubuce a kansu kamar, "Mutane na fama da yunwa da rashin aikin yi, suna kuma cikin fushi."

Wasu kwalayen kuma an rubuta, "Ba zai yiwu a ce an bambanta hukuncin da ake wa talakawa da masu arziki ba."

Kungiyar da ke jagorantar zanga-zangar mai suna Enough is Enough, ta ce ta fito ne domin nuna damuwa a kan al'amuran da suke damun jama'a kamar rashin tsaro da tabarbarewar bangaren ilimi da na lafiya da rashin wutar lantarki da kuma rashin aikin yi.

Rahotanni daga birnin Fatakwal da ke jihar Rivers na cewa mutane sun fara fitowa don yin zanga-zangar.

Ko a Abuja ma babban birnin kasar, rahotanni na cewa tsirarun mutane sun fara taruwa a dandalin Unity Fountain don gudanar da zanga-zangar.

Dalilin zanga-zangar

Tun da fari dai wani fitaccen mawaki a kasar 2Face Idibia ne ya yi kira ga mutane da su mara masa baya a zanga-zangar da ya so gudanarwa a ranar Litinin din a biranen Abuja da Lagos.

Sai dai jami'an tsaro sun taka masa birki tare da barazanar kama shi, saboda a cewarsu sun samu bayanan sirri cewa zanga-zangar za ta janyo hargitsi.

Wannan dalili ne ya sa mawakin ya janye daga aniyar tasa, amma sai kungiyoyin fararen hula suka ce za su ci gaba da ita 'ba gudu-ba-ja-da-baya.'

Sharhi

Masu sharhi dai na ganin akwai matukar wahala wajen hado kan mutane su yi zanga-zanga a ranar Litinin da kowa ke kokarin tafiya wajen aiki, musamman a birni irin Lagos mai cunkoson jama'a.

Sai dai duk da haka rashin yawan masu gudanar da zanga-zangar ba zai boye gaskiyar halin da mutane ke ciki ba na matsin tattalin arziki da hauhawar farashin kayayyaki, da kuma yadda mutane ke ganin gwamnati ba ta daukar matakin da suka dace don magance matsalar.

Masana tattalin arziki na cewa babu ayyukan yi kuma hauhawar farashin ya sa mutane cikin halin ka-ka-ni-ka-yi.

'Yan kasuwa da masu masana'antu na korafi kan manufofin gwamnati da suke ganin ba su da tasiri , musamman wajen musayar kudaden kasashen waje, abin da ya sa lamarin ke kara tabarbarewa.