Ana samun yawaitar mutuwar masu tabin hankali a Birtaniya

Ingila
Image caption Masu fama da tabin hankali na fuskantar barazanar mutuwa

Alkaluman Cibiyar Kula da Masu Tabuwar Hankali ta Ingila na nuna cewa yawan marasa lafiyar da ke mutuwa ya karu da kashi 50 cikin 100 , a shekara uku.

Kididdigar wadda shirin BBC Panorama, gano ya dogara ne a kan wani sakamakon bincike da aka samu ta hanyar 'yancin samun bayanai daga cibiyar kula da masu tabuwar hankalin.

Yawancin marasa lafiyar na mutuwe ne sakamakon kisan kai da rashin kulawa da kuma rashin jin dadin rayuwa.

Cibiyar kiwon lafiya ta Birtaniya ta bayyana cewa ana sa ran cewa kididdigar ka iya karuwa.

Cibiyoyin kula da masu tabin hankali 33 daga cikin 57 a Ingila sun amsa neman bayanan da shirin Panorama ya bukata.

Tsakanin shekarar 2012 zuwa 2013, cibiyar ta bayyana rahoton mutuwar mutane 2,067 wadanda ke da tabuwar hankali da ba a zata ba.

Sai dai kuma tsakanin 2015 zuwa 2016 alkaluman mamatan sun karu zuwa 3,160.

An samu wannan karuwa ne a lokacin da aka rage kudaden da ake bai wa cibiyar, wadda ke bai wa mafiya yawan masu fama da tabuwar hankali, kiwon lafiya, a Ingila.

Sabon bincike na tsarin Panorama daga Asusun kiwon lafiya ya nuna cewa an rage kudaden da ake bai wa cibiyar kula da masu tabin hankali.

Ana bai wa cibiyar dai kudaden da yawansu ya kai Fam milliyan 150 cikin sheraru hudu, idan aka kwatanta da kudaden da kasar ke bukata a fanin kiwon lafiya wato Fam biliyan takwas.

Labarai masu alaka