China ba ta amince da takunkumin Amurka kan Iran ba

China

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kasar Sin ba ta amince da takunkumin Amurka ba

Kasar China ta nuna rashin amincewarta a kan sabon takunkumi da gwamnatin Trump ta sanya wa Iran, da cewa hakan zai shafi harkokin kasuwancinta.

Kamfanoni biyu na kasar China da wasu hamshakan mutane uku na cikin jerin sunaye da Jami'an Amurka ke zargi da mai da hankali a kan cibiyar kasuwancin makamai na Iran.

Kakakin ministan kula da harkokin waje a birnin Beijing, Lu Kang ya ce, "Sanya takunkumi a kan wasu kamfanoni uku ba zai taimaka ba."

Wannan shi ne takunkumi na farko da shugaba Donald Trump ya sanya wanda aka bayar da sanarwarsa a ranar Juma'a, bayan Iran din ta yi gwaje-gwajen makami mai linzaminta.