Ana zargin malaman katolika da lalata yara

Babban malamamin cocin Katolika na Australia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Cardinal George Pell shi ne babban malamin cocin Katolika da ke kasar Australiya

Wani bincike da aka yi a kan yin lalata da ake yi da yara a Australiya ya gano cewa an zargin kashi bakwai cikin 100 na malaman katolika sun lalata yara a tsakanin shekarun 1950 da 2010.

A wata cocin, an yi zargin kashi 40 cikin 100 na mabiyanta da aikata hakan.

Wata hukuma da ke neman mafita kan yadda za a magance cin zarafin yara ta ce, an shaida mata cewa sama da mutane 4,440 sun yi ikirarin cewa an yi lalata da su tsakanin shekarar 1980 zuwa 2015.

Hukumar wacce ke kan gaba wajen binciken, tana kuma bincike a kan lalatar da ake yi da yara a wasu wuraren wanda ba na addini ba.

Hukumar ta ji labarai masu ban tsoro daga wadanda malaman coci suka yi lalata da su.

Daya daga cikin yaran da a ka ci zarafinsu ya ce wani malamin cocin katolika ya yi lalata da shi a aji, inda kuma ya umurci ragowar dalibai da su kawar da kawunansu.

Binciken ya kuma ji labarin wata yarinya da wani malamin cocin ya yi mata barazana da wuka kuma yasa yara suka rika zama a tsakanin cinyoyinsa.