Me ya sa mai suna Muhammad ke wahalar samun aiki a Turai?

Mutanen biyu sun nemi aiki a wuri 100
Bayanan hoto,

Adam da Mohamed suna da karatu iri da gogewa iri daya

Wani bincike da BBC ta yi ya gano cewa masu neman aiki wadanda sunansu na Turawa ne ko kuma Kiristanci suna samun aikin fiye da masu sunan Musulunci.

Wani misali kan hakan shi ne yadda wasu mutum biyu masu neman aiki wato "Adam" da "Muhammad", wadanda kuma suke da shaidar karatu da gogewa iri daya, suke nemi aiki a wurare 100.

To amma Adam ya samu gayyatar rubuta jarrabawar aiki 12 daga cikin 100 da ya nema, a inda shi kuma Muhammad ya samu gayyata daga wuri hudu kacal.

Wannan binciken dai ya nuna cewa Musulmai a Burtaniya na fuskantar wariya a ayyuka sabanin sauran mabiya addinai.

Wani farfesa a jami'ar Bristol ta Birtaniya, Farfesa Tariq Modood, ya yi nazarin wannan binciken na BBC.

Ya ce, "Abin da muka gano karara shi ne duk wanda takardarsa ta neman aiki take dauke da suna mai lafazin Musulunci, to watakila ya samu gayyatar rubuta jarrabawar daukar aiki guda daya daga cikin ukun da ya nema."

Ya kara da cewa a birni kamar London "Akwai rabuwar kai sosai, kuma al'amarin wariya ya yi muni fiye da yadda na zata a birnin."

Kidayar jama'a da aka yi a 2011 a Burtaniya, ta nuna cewa yawan Musulmi a London ya fi miliyan daya cikin mutane miliyan takwas da dubu dari biyu na mazauna birnin.

Wani bincike da Majalisar Musulman Burtaniya ta yi ya gano cewa fiye da rabin Musulman suna fama da kangin talauci fiye da sauran mabiya addinai ko kuma al'ummar da ke zaune a birnin na London.

Bayanan hoto,

Fuskokin Musulmai mata a Turai

Barista Nabila Mallick tana wakiltar Musulamai wajen daukar mataki kan nuna wariya a wajen aiki.

Ta ce, "Akwai fahimtar da wasu ke da ita cewa ma'aikata Musulmai ba su da ladabi kuma suna shiga harkokin siyasa sannan kuma ana yi wa irin tufafin da suke sanyawa kallon na masu tsaurin addini."

"Hakan kuma yana taimakawa sosai wajen nuna wa Musulmai wariya a fannonin daban-daban na rayuwar aiki."