'Mun yi imanin Buhari ne kadai zai iya ceto Najeriya'

Magoya bayan Buhari
Bayanan hoto,

Masu zanga-zangar goyon bayan gwamnatin shugaba Buhari

Yayin da a biranen Abuja da Legas da Fatakwal daruruwan 'yan Najeriya suka yi dafifi domin gudanar da zanga-zangar nuna bacin rai kan halin 'matsin tattalin arzikin' da suka ce kasar na fuskanta, wani gungun magoya bayan shugaba Buhari, mai suna 'Buhari Network Group', ya yi tasa zanga-zangar domin nuna goyon baya dari bisa dari ga gwamnati.

Masu zanga-zangar sun ce kasa kamar Najeriya na bukatar shugaba mai gaskiya wanda kuma zai dora kasar a kan turba, a saboda haka Buhari ne ya cancanci wadannan siffofi.

Buhari Network Group ta ce ya kamata masu nuna kin jinin gwamnatinsa su san cewa babu wata kasa da za ta cigaba ba tare da fuskantar matsin tatttalin arziki irin wanda Najeriya ke fuskanta yanzu ba.

Dangane kuma da nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu, masu goyon bayan gwamnatin sun ce yaki da Boko Haram babbar nasara ce da ko ita kadai ta isa ta wanke shugaba Buhari.

Sun yi kira ga 'yan Najeriya cewa ya kamata su yi karatun ta-nutsu wajen tantance tsaki da tsakuwa musamman dangane da rikicin Boko Haram, a baya da a yanzu.

Bayanan hoto,

Da fari tsirarun mutane ne suka fara taruwa a filin wasa da ke Lagos

Daruruwan mutane ne dai suka gudanar da zanga-zanga kan matsin tattalin arzikin da kasar ta samu kanta a ciki da kuma hauhawar farashin kayayyaki, da safiyar ranar Litinin.

Tun da safiyar ne dai mutane suka fara taruwa a filin wasa na birnin Lagos, wurin da aka baza jami'an 'yan sanda.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wakilin BBC ya ce, "Da fari dai jami'an 'yan sandan da aka zuba sun fi masu zanga-zangar yawa, amma daga bisani mutane sun karu har yawansu ya kai daruruwa."

Mutane suna dauke da kwalaye da aka yi rubuce-rubuce a kansu kamar, "Mutane na fama da yunwa da rashin aikin yi, suna kuma cikin fushi."

Wasu kwalayen kuma an rubuta, "Ba zai yi wu a ce an bambanta hukuncin da ake wa talakawa da masu arziki ba."

Kungiyar da ta jagoranci zanga-zangar mai suna Enough is Enough, ta ce ta fito ne domin nuna damuwa a kan al'amuran da suke damun jama'a kamar rashin tsaro da tabarbarewar bangaren ilimi da na lafiya da rashin wutar lantarki da kuma rashin aikin yi.

Rahotanni daga birnin Fatakwal da ke jihar Rivers sun ce can ma an yi zanga-zangar.

A Abuja ma, babban birnin kasar, an gudanar da zanga-zangar.

Dalilin zanga-zangar

Tun da fari dai wani fitaccen mawaki a kasar 2Face Idibia ne ya yi kira ga mutane da su mara masa baya a zanga-zangar da ya so gudanarwa a ranar Litinin din a biranen Abuja da Lagos.

Sai dai jami'an tsaro sun taka masa birki tare da barazanar kama shi, saboda a cewarsu sun samu bayanan sirri cewa zanga-zangar za ta janyo hargitsi.

Wannan dalili ne ya sa mawakin ya janye daga aniyar tasa, amma sai kungiyoyin fararen hula suka ce za su ci gaba da ita 'ba gudu-ba-ja-da-baya.'

Sharhi

Masu sharhi dai na ganin akwai matukar wahala wajen hado kan mutane su yi zanga-zanga a ranar Litinin da kowa ke kokarin tafiya wajen aiki, musamman a birni irin Lagos mai cunkoson jama'a.

Sai dai duk da haka rashin yawan masu gudanar da zanga-zangar ba zai boye gaskiyar halin da mutane ke ciki ba na matsin tattalin arziki da hauhawar farashin kayayyaki, da kuma yadda mutane ke ganin gwamnati ba ta daukar matakin da suka dace don magance matsalar.

Masana tattalin arziki na cewa babu ayyukan yi kuma hauhawar farashin ya sa mutane cikin halin ka-ka-ni-ka-yi.

'Yan kasuwa da masu masana'antu na korafi kan manufofin gwamnati da suke ganin ba su da tasiri , musamman wajen musayar kudaden kasashen waje, abin da ya sa lamarin ke kara tabarbarewa.