Ba zan taɓa lamuntar jawabin Trump ba - Bercow

John Bercow

Asalin hoton, AFP/PRU

Bayanan hoto,

John Bercow ya ce sai dai idan abin ya fi ƙarfinsa kafin shugaba Trump ya samu damar yin jawabi a gaban majalisar wakilan Burtaniya

Shugaban majalisar wakilan Burtaniya John Bercow ya ce zai yi "kakkausar suka" ga gayyatar shugaban Amurka Donald Trump don yin jawabi a gaban zauren majalisar yayin ziyarar da zai kai.

John Bercow ya faɗa wa 'yan majalisar cewa "adawa da wariyar launin fata da ta jinsi, babban tunani ne".

'Yan majalisa daga jam'iyyar SNP sun tafa wa shugaban bayan jawabinsa.

An gayyaci shugaba Donald Trump zuwa Burtaniya bayan ganawarsa da Fira minista Theresa May cikin watan jiya a birnin Washington.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An gayyaci Donald Trump zuwa Burtaniya ne bayan ganawarsa da Fira minista Theresa May a Washington

A ranar 20 ga watan Fabrairu ne, 'yan majalisar za su tafka muhawara kan wani ƙorafi da ke neman Burtaniya ta janye gayyatar da ta yi wa Trump, bayan mutum miliyan ɗaya da dubu 800 sun rattaba hannu.

John Bercow ya faɗa wa 'yan majalisar cewa yin jawabi a gaban majalisar dattijai da wakilan ƙasar "wata daraja ce da mutum ke samu" amma ba "'haƙƙi ne" ba.

'Ba da yawuna ba'

Ya ce yana ɗaya daga cikin mutum uku da ke riƙe da "mukullan" zauren Westminster, a cewarsa "Ko kafin haramta wa baƙi shiga Amurka, Ni da kaina zan yi kakkausar suka kan buƙatar shugaba Trump ya gabatar da jawabi a gaban zauren Westminster."

"Bayan ya haramta wa baƙi shiga (ƙasarsa) sai na ƙara kausasa adawata kan gayyatar shugaba Trump a gaban zauren."

Shugaban majalisar ya kuma ce "Muna mutunta dangantakarmu da Amurka, amma idan wannan ziyara ta tabbata, to ba da yawuna ba."

Wata mai magana da yawun shugaban majalisar dattijai ta ce: "Mr Bercow bai tuntuɓi shugaban majalisar dattijai ba a kan wannan jawabi nasa."