Fitsarin kwance ya janyo mutuwar wani yaro a Faransa

French Police

Asalin hoton, AFP/GETTY IMAGES

Bayanan hoto,

Wasu daga cikin raunukan da aka gano a kan yaron, na da alaƙa da cin zarafi

Wasu ma'aurata a Faransa sun shiga hannu a kan mutuwar ɗansu mai shekara biyar da suka ladaftar saboda ya malala fitsarin kwance.

An gano gawar yaron a kusa da wata magudanar ruwa cikin wani yanki da ke arewacin Faransa a daren ranar Lahadin da ta gabata.

Mahaifiyarsa da kuma mijinta sun ce sun sanya yaron falfalawa da gudu a waje cikin sanyi ba tare da tufafin kirki a jikinsa ba.

Mai shigar da ƙara Patrick Leleu ya ce binciken gawar yaron da aka yi ya gano raunuka da dama a kansa.

Ya ce wasu daga cikin raunukan mai yiwuwa yaron ya ji su ne sakamakon faɗuwa, amma wasu ga alama cin zarafinsa aka yi da gangan.