Wata tsutsa ta auka wa gonakin masara a Afirka

Maize

Asalin hoton, Cabi

Bayanan hoto,

Tsutsar tana lalata totuwar masara

Masana kimiyya sun buƙaci ɗaukar matakin gaggawa don kawo ƙarshen yaɗuwar wata tsutsa da ke lalata masara wadda ke ci gaba da bazuwa cikin sauri a faɗin Afirka.

Tsutsar wata babbar barazana ce ga ƙoƙarin wadata ƙasa da abinci da kuma cinikin amfanin gona, kamar yadda cibiyar bunƙasa noma da kimiyyar halittu ta duniya (Cabi) ta yi gargaɗi.

Ta ce hanyar samun kuɗin shiga ga manoma tana fuskantar hatsari a lokacin da wata baƙuwar tsutsa ke barazanar shiga nahiyar Asiya da tekun Mediterranean.

Hukumar samar da abinci da aikin gona ta duniya na shirin gudanar da wani taron gaggawa a kan wannan batu.

Tsutsar wadda ake kira armyworm, saboda tana cinye duk tsiron da ta samu a kan hanyarta a lokacin da take kusantar amfanin gona, an san ta a Amurka ta arewa da ta kudu amma a bara ne aka fara gano ta a nahiyar Afirka.

Babban jami'in cibiyar Cabi Dr Matthew Cock ya ce: "Waɗannan tsutsotsi masu mamaya a yanzu sun zama babbar barazana da ke yaɗuwa cikin sauri a yankin ƙasashe masu zafi na Afirka da kuma yiwuwar bazuwa zuwa Asiya.

Asalin hoton, Cabi

Bayanan hoto,

Tsutsar tana lalata totuwar masara

Masana kimiyya na tsammanin tsutsar ko ƙwayayenta sun shiga Afirka ne ta hanyar amfanin gona da aka yi safararsa.

Da zarar sun sauka a wani yanki, balagaggun ƙwarin suna iya tashi su yi tafiya mai nisa don bazuwa cikin sauri.

Dr Jayne Crozier, ta cibiyar Cabi, ta ce an tabbatar da wanzuwar wannan tsutsa a Afirka ta yamma kuma ana jin akwai ta a kudanci da gabashin nahiyar, yankuna da dama da suka dogara da masara a matsayin cimar gidan kowa.

Ta faɗa wa BBC cewa "Ga alama tsutsar ta kasance a can tsawon wani lokaci kuma tana haddasa matuƙar ɓarna a yanzu."

Hukumar samar da abinci da aikin gona za ta gudanar da taron gaggawa a birnin Harare daga ranar 14 zuwa 16 ga watan Fabrairu don yanke shawara a kan martanin da za a mayar wajen tunkarar barazanar tsutsar.

Ta ce an tabbatar da ganin tsutsar a Zimbabwe sannan kuma rahotannin farko-farko sun ce tana iya yiwuwa akwai ta a ƙasashen Malawi da Mozambique da Namibia da Afirka ta kudu da Zambia.

Wani bincike da Cabi ta gudanar ya tabbatar da kasancewar tsutsar a Ghana.