Kasashen Sahel sun amince da kafa rundunar yaki da ta'addanci

Kasashen yankin Sahel za su kafa rundunar hadin gwiwa domin yakar ta'addanci

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Kusan mutane 80 aka kashe a wani hari da aka kai Gao na arewacin Mali

Kasashe biyar na Afirka sun amince da kafa wata rundunar yaki da ta'addanci ta hadin gwiwa a yankin Sahel.

An sanar da wannan mataki ne a wajen wani taron kolin kasashen da ake kira G5 da suka hadar da Mali da Chadi da Nijar da Burkina Faso da kuma Mauritania.

Taron ya biyo bayan wani hari da aka kai cikin watan jiya a birnin Gao na arewacin Mali wanda ya yi sanadin mutuwar kusan mutum tamanin.

Shugaban kasar Nijar, Muhammadou Issoufou ya ce za a bukaci amincewar kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya kafin kafa rundunar.

Babu cikakken bayani a kan ko adadin dakaru nawa ne za su kasance a cikin rundunar.