Isra'ila ta sake yi wa Palasdinawa ƙwace

Kasashen duniya sun caccaki Isra'ila kan matakin da ta dauka.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kasashen duniya sun caccaki Isra'ila kan matakin da ta dauka.

Majalisar dokokin Isra'ila ta amince da wani kudurin doka mai cike da ce-ce-ku-ce, wanda ya bayar da umarni a gina wa Yahudawa sabbin gidaje dubu hudu a fulotai mallakin Palasdinawa da ke yammacin kogin Jodan.

'Yan majalisar dokoki 60 ne suka amince da dokar, yayin da 52 suka yi fatali da ita.

Dokar ta ce za a bai wa Paladinawa fansa ta kudi ko kuma wasu fulotan amma ba a yankin ba.

Sabon shugaban Amurka Donald Trump ba ya daukar matakai masu tsauri a kan Isra'ila game da gine-ginen da take yi a yankunan Palasdinawa sabanin wanda ya gaba Barack Obama, duk da sukar da matakin ke sha daga kasashen duniya.

Isra'ila ta soma gina sababbin dubban matsugunan Yahudawa ne a makonnin da suka wuce bayan da ta tabbatar cewa sabuwar gwamnatin Amurka na goyon bayanta.

Zaman doya-da-manja

Palasdinawa sun ce sabuwar dokar ta yi kafar-ungulu ga yunkurin samar da zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu, sannan ta kawo cikas a game da fafutikar da suke yi ta samun kasar kansu.

Mai magana da yawun shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas, Nabil Abu Rudeineh, ya ce "Matakin zai tsawaita daman doya-da-manjan da ake yi sannan ya kawo rudani".

Tuni dai Antoni Janar na Isra'ila, Avichai Mandelblit, ya ce dokar ta saba wa kundin tsarin mulkinsu kuma ba zai kare ta a kotun kolinsu ba.

Manzon majalisar dinkin duniya a Gabas Ta Tsakiya, Nickolay Mladenov, ya ce kuri'ar da majalisar dokokin Isra'ilan ta kada ta saba wa doka, yana main cewa "za ta yi katsalandan ga samun zaman lafiya tsakanin Larabawa da Isra'ila".