Boren sojoji ya bazu a Ivory Coast

Ivory Coast

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Boren sojoji ya bazu Ivory Coast

Tawagar gwamnatin Ivory Coast ta na hanya domin saduwa da sojoji da suka yi bore ta hanyar harbin iska, a wani barikin soja.

An yi harbe-harben ne a Talata a wani sansanin sojoji da ke Kudu maso gabashin yankin Adiake.

An rufe wurin kasuwanci da makarantu sannan kuma mazauna kasance a cikin gidajensu.

Sojoji na wannan bore ne domin gwamnati ta cika nata alkawarin data yi na biyan su kudaden alawus-alawus.

Tun dai watan Janairu sojoji suke irin wannan bore a biranen kasar bisa zargin rashin biyan su kudaden.

Wannan boren sojoji ya fara a tsakiyar birnin Bouake amma yanzu kuma ya bazu a kasar baki daya.