An kashe dubban mutane a kurkukun Syria — Amnesty

Amnesty

Asalin hoton, Amnesty International

Bayanan hoto,

Kungiyar Amnesty ta ce akwai mutane kusan 20,000 a gidan yarin Saydana

Wani bincike ya gano cewa an kashe kimanin mutum dubu 13 a asirce a gidan yarin kasar Syria.

Kungiyar Amnesty international wadda ta bayar da rahoton ta ce, mafi yawan mutanen fararen hula ne masu goyon bayan abokan hamayyar gwamnatin kasar.

Amnesty ta kuma yi zargin cewa a ko wanne mako ana kashe mutane ta hanyar rataya a gidan yarin Saydnaya, tun tsakanin watan Satumbar 2011 zuwa watan Disambar 2015.

Kungiyar kare hakkin bil'adaman ta kara da cewa umarnin kisan na zuwa ne daga gwamnatin Syria.

Sai dai a baya gwamnatin ta sha musa zargin kashe ko gallazawa fursunoni.

Haka kuma, kwararru kan kare hakkin dan adam na Majalisar Dinkin Duniya sun ce, shekara daya da ta gabata an samu hujjoji da suka tabbatar da cewa ana kashe dubban mutanen da ake tsare da su a gidan yarin.