Ko kun san halin da kasuwar kifi ta Maiduguri ke ciki?

Hotunan da tawagar BBC ta dauko na yadda al'amura ke gudana a babbar kasuwar kifi ta Baga da ke jihar Borno a Arewacin Najeriya, tun bayan da rikici ya yi kamari a yankin.

Baga Fish Market
Bayanan hoto,

Kasuwar kifi ta Baga babbar kasuwa ce da ake hada-hadar saye da sayar da kifi a jihar Borno, kuma ana zuwa daga kasashe daban-daban na Afirka.

Bayanan hoto,

Kasuwar ta kai shekara 38 da kafuwa, inda kasashe irin su Kamaru da Nijar da Chadi da Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka ke zuwa domin sarin kifi.

Bayanan hoto,

Sai dai tun bayan da rikicin Boko Haram ya yi kamari, al'amura suka ja baya a kasuwar, sannan kuma janyewar ruwan tafkin Chadi ma, inda a can ake samo mafi yawan kifin, ya taka rawa wajen durkushewar kasuwar.

Bayanan hoto,

A ziyarar da tawagar BBC ta kai kasuwar ta Baga, ta ga yadda a yanzu harkoki ba sa tafiya yadda ya kamata. "A da za a ga tireloli suna lodi, amma yanzu wajen ya zama kusan wayam sai abin da ba a rasa ba."

Bayanan hoto,

A baya irin bunksar da kasuwar ke da shi ya sa har al'ummar Kudancin Najeriya na zuwa. Sai dai yanzu a iya cewa sai 'yan tsiraru kawai ake gani daga cikinsu.

Bayanan hoto,

Akwai mata da dama Bare-bari da ke zuwa kasuwar inda suke sayen burbushin kifi daga wajen manyan diloli suke sayarwa ga masu bukatarsa.

Bayanan hoto,

Sun shaida wa BBC cewa ba za su iya daina wannan sana'a ba domin daga cikinta suke rufawa kansu asiri.

Bayanan hoto,

Ba ya ga kifi kuma ana sayar da naman kananan dabbobin daji da aka fi sani da Bush meat, kala-kala a kasuwar. Wani dan Kudancin Najeriya ya shaida wa BBC cewa, "Ana cinikinsu sosai."

Bayanan hoto,

A yanzu haka daruruwan matasa da dattijan da a baya ke samun rufin asiri a kasuwar a yanzu haka kusan za a ce zaman kashe wando suke yi, duba da yadda komai ya ja baya.

Bayanan hoto,

"Ba abin da za mu ce sai godiyar Allah tunda dai muna da rai da koshin lafiya, amma batun ciniki kam ya ja baya sosai." Inji wasu dattijai da ke kasuwar.

Bayanan hoto,

Ita dai wannan kasuwa a cikin garin Maiduguri take, amma ana kiranta Baga Fish Market saboda a garin Baga ake babbake kifin ake kawo shi kasuwar.