'Yan Maiduguri na shan wahalar cire albashi a ATM

A Najeriya, bisa al'ada ma'aikata kan yi murna duk lokacin da aka kai karshen wata, saboda za a biya su albashi. Amma a birnin Maiduguri da ke Arewa maso Gabashin kasar lamarin ba haka yake ba.

Ma'aikata da dama kan yi fargabar dogon layin da su kan yi wajen cirar kudi daga injinun ATM.

Ibrahim Isa ya ziyarci wasu bankuna a titin Sir Kashim Ibrahim da ke birnin, ga kuma rahoton da ya aiko mana.