Kamfanin Twitter zai dau mataki kan cin zarafin mutane

Twitter

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Twitter zai kawo sauye-sauye don kare cin zarafin mutane

Kamfanin Twitter ya sanar da sabbin matakai guda uku, da ya ce, za su taimaka wajen rage cin zarafi ko keta mutuncin mutane a kafafen sadarwa na zamani.

Ya ce matakan za su hana mutane bude sabbin shafuka idan har aka rufe shafinsu na ainihi da suka keta mutuncin wasu mutane a kai.

Kamfanin kuma zai kirkiro wata dabara ta goge duk wasu bayanai da ake ganin na cin zarafin wasu ne.

Twitter ya kara da cewa masu sharhin kamfanin suna aiki domin tabbatar da cewa ba a saurin lalubo kalaman cin zarafi ko mayar da martani mara ma'ana, a shafin.

Kamfanin na Twitter dai ya ce nan da makonni kadan masu zuwa ne za a sake samar da wasu sauye-sauyen da za su taimaka wajen kare hakkin fadin albarkacin baki.

A kowane wata dai mutane miliyan 317 ne ziyartar shafin na Twitter, a karshen shekarar 2016.

A watan Maris na 2006 ne dai aka kirkiri kamfanin na Twitter, a Amurka.