Kun taba ganin hoton mutum 500 na dangi daya?

China Family Re-union

Asalin hoton, ZHANG LIANGZONG

Bayanan hoto,

'Yan zuri'ar sun zo taron ne daga biranen Beijing da Shanghai da Xinjiang da kuma kasar Taiwan

Fiye da mutum 500 'yan zuri'a daya a China sun dauki hoto a tare, a wani al'amari da ba a saba gani ba.

An dauki hotunan ne a wani taron haduwa da juna da iyalan suka shirya a kauyen Shishe da ke gundumar Zhejiang a Gabashin China.

Dangin sun yi taron ne a makon da ya gabata lokacin bikin sabuwar shekarar kasar, wadda mutane ke shirya liyafar cin abinci tare da zuri'arsu.

Mai daukar hoto Zhang Liangzong ya dauki hoton wannan zuri'a ne da jirgi marar matuki a gaban wani dutse kusa da kauyen Shishe.

Ya shaida wa BBC cewa tushen zuri'ar Ren ya samo asali ne tun shekaru 851 da suka gabata, sai dai zuri'ar ta shafe shekaru 80 ba su san yawan su da yaduwarsu ba.

A baya-bayan nan ne dattijan kauyen suka fara samar da bayanai kan iyalan zuri'ar inda suka yi kokarin gano mutum 2,000 da suke raye, daga iyalai bakwai daban-daban na zuri'ar wadanda duk tushensu daya.

A don haka suka hada wannan gagarumin taro, inda suka yi kokarin hado kan mutum 500 daga cikinsu.