An hana sallah a kan titi a jamhuriyyar Benin

Patrice Talon

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaba Talon ya ce ba adawa da Musulunci ce ta sa aka dauki matakin ba

Hukumomi a jamhuriyyar Benin sun ce ba za su sauya matakin da suka dauka na hana Musulmai sallah a kan titi ba.

Amma bayan tattaunawa da wasu shugabannin addini, shugaban kasar Patrice Talon ya amince gwamnati za ta samar da tallafin kudi domin a gina karin masallatai.

Kantoman birnin Cotonou ya ce an dauki wannan mataki ne sakamakon wani al'amari da ya faru a ranar Juma'a da rana, inda mutane suka baza shimfidu ta ko ina a kan tituna don yin sallar Juma'a.

Al'amarin da ya wo cunkoson mutane da na ababen hawa.

Sai dai 'yan majalisar dokoki Musulmai da malaman addinin Musulunci sun ce hana sallah a kan titi nuna bambanci ne ga al'ummarsu.

Amma shugaba Talon ya ce matakin ba ya nufin adawa da Musulunci, sai dai kokarin tabbatar da cewa babu cunkoso a biranen kasar da kuma karfafa tattaln arziki.

An yi amanna cewa kashi 25 cikin 100 na mutanen kasar Musulmai ne.

A wata alama ta cimma yarjejeniya, ministan harkokin cikin gida na Benin Sacca Lafia, ya ce za a ci gaba da sallar Juma'a a kan titi kafin a kammala gina karin masallatan, in dai har ginin ba zai dauki dogon lokaci ba.