Me ya sa Kamaru ta toshe intanet?

Mutane a wurin yin amfani da intanet

Asalin hoton, Twitter

Bayanan hoto,

Rashin intanet a Kamaru ya shafi bankunan kasar da dama

Makonni uku bayan rahotanni sun bayyana cewa an toshe intanet a bangarorin Kamaru da ke yaren Ingilishi, mazauna yankunan sun ce har yanzu intanet din bai dawo ba.

Ko me yasa?

'Yan Kamaru suna zargin katse kashi 20 cikin 100 na mutane daga samun intanet din wani mataki ne irin na kasashen waje da gwamantin kasar ta dauka.

Lardunan Kudu maso Yammaci da Arewa maso Yammaci wadanda lamarin ya shafa sun yi ta zanga-zangar kyamar gwamnati a watannin baya-baya nan.

Kwana guda kafin daukewar intanet din ne ma'aikatar sadarwar kasar ta fitar da sanarwa inda ta yi gargadi ga masu amfani da kafafen sada zumunta cewa za ta dauki hukunci kan aikata miyagun laifuka.

Ma'aikatar ta ce zata yi hakan ne idan har masu amfani da kafafen sada zumunta suka yada wasu bayanai ba tare da wasu hujojji ba.

Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa hukumomin sun aike da sako ta wayoyin mutane, inda suka sanar da irin hukunci tare da dogon wa'adi da mutum zai shafe a gidan kaso idan har ya yada labaran karya a kafafen sada zumunta.

'Yan Kamaru da dama sun dauki hoto tare da wallafa gargadin da aka aika musu ta wayar tarho a shafin Twitter.

Babu wani bayani a hukumance tun bayan da aka dakatar da intanet ko kuma rahoto a kan lalacewar wani abu, wanda ya sa 'yan kasar suka yanke shawarar cewa yin hakan wani yunkuri ne na gwamnati na hana mutane damar bayyana ra'ayoyinsu.

Me ya sa yankunan da ake Ingilishi kawai abin ya shafa?

Bayanan hoto,

Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma su ne yankuna biyu da ke yaren Ingiglishi a Kamaru

Hakan ya faru ne tun bayan tashe-tashen hankulan da yankunan da ke yaren Ingilisihi suka yi, da kuma kullatar gwamanti wanda hakan ya jawo zanga-zanga da yajin aiki.

Masu zanga-zangar na cewa 'yan Kamaru masu Faransanci wadanda suka fi yawa na nuna wariya ga 'yan tsirarun da ke Ingilishi.

A watan Nuwambar bara ne dai aka kama sama da mutane 100 aka kuma harbe mutum guda har lahira a wata zanga-zanga a kan tilasta amfani da Faransanci a kotu da makarantu na yankunan da ke Ingilishi.

Lauyoyi da malamai sun tafi yajin aiki a watan Nuwamba a garin Bamenda a kan batun wanda hakan ya sa garin ya kasance ba hada-hada.