Fasto ya bai wa mabiyansa gubar bera domin gwada imaninsu

Light Monyeki

Asalin hoton, Twitter

Bayanan hoto,

Akasarin malaman cocin a Afirka ta kudu na abubuwa da dama da ke jawo cece kuce a cikin al'umma

Wani malamin coci a kasar Afirka ta kudu ya bai wa mabiya cocinsa maganin bera domin gwada imaninsu a cewar rahoton da kafar yada labarai na eNCA ta kasar ta fitar.

Light Monyeki, shi ne ke shugaban cocin Grace Living Hope, da ke Pretoria babban birnin kasar.

Light ya ce shan gubar alama ce ta nuna cewa mutuwa ba ta da iko a kansu.

Wasu hotunan da ya wallafa a shafinsa na Facebook, sun nuna yadda yake narkar da maganin kashe bera kafin ya kurba sannan daga bisani ya rika bai wa 'yan cocin.

Mista Monyeki shi ne malamin coci na baya-bayan nan da ya aikata abubuwa masu cike da sarkakiya.