An gurfanar da sojoji kan cin zarafin nakasasshe

Sanarwar wadda kakakin rundunar Birgediya Janar Sani Usman Kuka-Sheka ya sanya wa hannu, ta ce 'cin zarafin dan adam ba ya cikin aikin soji.'
Rundunar sojin Najeriya ta ce an jawo hankalinta kan wani bidiyo da ke nuna yadda wasu sojoji biyu suke zaluntar tare da azabtar da wani nakasasshe saboda ya sanya wata riga irin ta sojoji.
A wata sanarwa da ta fitar, rundunar sojin ta ce lamarin ya faru ne a ranar Talatar da ta gabata, a garin Anacha da ke jihar Anambra a Kudancin Najeriya.
Sanarwar ta ce tuni aka gano su waye sojojin aka kuma kama su, a kokarin da rundunar sojin ke yi na kin lamauntar duk wani halin rashin da'a da rashin kwarewar aiki, musamman ma abin da ya shafi take hakkin dan adam.
Ta kuma ce tuni aka fara tuhumar sojojin da laifin gallazawa farar hula.
Rundunar sojin ta kuma gargadi dakarunta da su guji aikata irin wadannan laifuka na keta hakkin dan adam da suke dakile darajar rundunar a idon al'umma.
"Don haka muna kira ga jama'a da kada su kalli abin da ya farun a matsayin aikin rundunar sojin, don ba haka take gudanar da al'amuranta ba," inji sanarwar.
Ko a makon da ya gabata ma rundunar sojin ta yankewa wani soja hukunci daurin shekara bakwai a gidan yari, bayan samunsa da laifin kisa ba da niyya ba.