An caccaki shugaban Kenya kan rawar Dab

Kenyatta

Asalin hoton, Uhuru Kenyatta Twitter

Bayanan hoto,

Shugaba Uhuru Kenyatta na neman goyon bayan mawaka don sake zabarsa

'Yan kasar Kenya sun yi ta ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta da muhawara, sakamakon wani bidiyo da aka nuna na shugaban kasar Uhuru Kenyatta yana rawar Dab lokacin da wata kungiyar mawaka ta kai masa ziyara a fadarsa.

A baya-bayan nan Mista Kenyatta yana yawan saduwa da fitattun mawaka da 'yan wasa a kasar, don neman hadin kansu a neman ci gaba da mulki da yake son yi.

Shugaban ya kuma fara yakin neman zabe a fadin kasar, inda yake kira ga matasa da su yi rijistar neman katin zabe kafin ranar 15 ga watan Fabrairu da za a rufe.

Mutane a kasar sun yi ta amfani da maudu'in '#DabOfShame,' inda suke sukar sa kan abin da ya yi na rawar Dab din, suna kuma zarginsa da cewa ya fi mayar da hankali kan yakin neman zabe fiye da kokarin warware matsalolin da kasar ke fuskanta, wadanda suka hada da yajin aikin da likitoci ke yi.

Sai dai masu goyon bayansa sun ce yin hakan na nuna cewa shugaban yana da saukin kai ne.