Ana tuhumar shugaban ENI da bayar da cin hanci a Nigeria

Mr Descalzi
Bayanan hoto,

Gwamnatin Italiya ce ta nada Mista Descalzi shugabancin kamfanin ENI

Masu shigar da kara a Italiya sun nemi alkali a kotun kasar da ya gurfanar da shugaban kamfanin man fetur na Enid da ake zargi da bayar da toshiyar baki a Najeriya.

Ana zargin Claudio Descalzi, da sayen wata rijiyar man fetur da ake zargin ta shafi cin hanci da karbar rashawa a shekara ta 2011 a kan kudin ya haura dala biliyan daya

An sayi rijiya ta hadin gwiwa tsakanin ENI da kuma wani kamfanin hako man fetur na Royar Dutch Shell, da shi ma a yanzu ake gudanar da bincike a kansa.

Babban abin da ake zargin kamfanonin biyu dai a yanzu shine, batun cewa suna sane a kan kudin da aka bayar da sunan biyan gwamnati, wata makarkashiya ce da aka shirya yadda kudin zasu fada zuwa aljihun wasu a matsayin bayar da toshiyar baki.

Sai dai dukkanin kamfanonin biyu sun musanta wannan zargi, inda suka yi tsayin daka da cewa sun biya kudin zuwa ga gwamnatin tarayya ne amma ba wasu mutane ba.

Sun nuna ko da hakan ta faru to basu da masaniyar wannan makarkashiya.

Kamfanin ENI dai ya ce yana bayan shugaban kamfanin Claudio Devalski dari bisa dari akan wannan lamari.

Binciken da ake gudanarwa a Italiya a yanzu dai yana daya daga cikin binciken da ake gudanarwa a kan sayen rijiyar man fetur a Najeriya da Holland.

A watan da ya gabata gwamnatin tarayyar Najeriya ta kwace wata rijiyar da ake hako man fetur, ta kuma bayar da umarni a dakatar da kwasar man fetur har sai bayan kammala binciken da ake yi cewa an bayar da toshiyar baki.