Gambia ba zata fice daga ICC ba

Gambia

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mr Barrow ya lashe zaben shugaban kasa

Shugaban kasar Gambia, Adama Barrow ya jaddada alkawarin da ya yi kafin zabensa cewa kasar ba za ta fice daga Kotun hukunta manyan laifuffukan yaki ta duniya (ICC) ba.

Yin hakan zai sauya shawarar da wanda ya gada, Yahya Jammeh ya yanke, inda ya ce, ''Kotun Turawa ce wadda aka kirkiro ta domin muzantawa da kuma hukunta wadanda ba Turawa ba, musamman ma 'yan Afirka."

Mista Barrow ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da babban jami'i na hukumar hadin kai da ci gaban kasa da kasa ta kungiyar tarayyar Turai, Neven Mimica, a Banjul babban birnin kasar.

A farkon watan Fabrairu ne kungiyar tarayyar Afirka ta sanar da ficewarta daga ICC.

Wani dan jarida dan Birtaniya a Gambiya ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa Kungiyar tarayyar Turai ta yi alkawarin kara taimakon kudi da take bai wa kasar Gambia.

Sai dai wasu kasashen nahiyar sun nuna cewa fita daga ICC ba aleri ba ne.

Mista Barrow dai ya lashe zaben shugaban kasar a ranar daya ga watan Disamba, a kan alkawarin kare 'yancin bil Adam, da ake sa ran zai kawo karshen danniya da 'yan Gambia suka fuskanta a lokacin mulkin Mr Jammeh, na shekaru 22.