An fasa rufe sansanin 'yan gudun hijira mafi girma a duniya

Sansanin dadaab

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Sansanin wanda aka samar a shekarar 1991 ya kai girman wani birnin

A shekarar da ta gabata ne dai gwamnatin Kenya ta bayar da umarnin rufe sansanin 'yan gudun hijira mafi girma a duniya wanda haka zai tirsasawa mutum dubu 260,000 komawa kasashensu.

A baya dai an dage wa'adin zuwa watan Mayu amma kuma wani alkalin kotun kolin kasar ya yanke hukuncin cewa shawarar da gwamnati ta yanke, dai-dai ya ke da cuzguna wa hakkin dan adam.

Sai dai gwmantin ta musanta zargin inda tace batu ne na tsaro ya sa ta daukar matakin.

Ta kara da cewa daga sansanin 'yan gudun hijirar ne ake shirya hare-haren da kungiyar al-shabab ke kai wa kasar.

A shekarar 1991 ne aka samar da sansanin Dadaab domin bai wa iyalai da suka tsere wa rikici a Somaliya muhalli, kuma wasu sun shafe sama da shekara 20 suna zaune a can.

Sai dai Hukumar kare hakkin bil adama ta kasar da wasu kungiyoyin sun kalubalanci hukuncin gwamnatin, inda suka ce hukuncin ya nuna wariya kuma ya sabawa dokar kasa da kasa.

Bayanan hoto,

Kungiyrar al-shabab ta kwace ikon wasu garuruwa a Somaliya

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty ta goyi bayan hukuncin kotun, inda ta ce wajibi ne a bisa doka Kenya ta kare mutanen da ke neman mafaka a sansanin.

Muthoni Wanyeki, wata ma'aikacin kungiyar ta ce, "Yau ranar tarihi ce ga miliyoyin 'yan gudun hijira wadanda a da ke cikin tararrabin mayar da su Somaliya, inda za su kasance cikin hadarin cin zarafi".

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Dadaab ne sansanin 'yan gudun hijira mafi girma a duniya

Masu tayar da kayar baya na al-Shabaab, suna ci gaba da kai munanan hare-hare a kasashen Kenya da Somaliya.