Gwamnatin Nigeria ta karbe ragamar kamfanin Arik

Jirigin saman Arik

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Gwamnatin Najeriya ta ce ta dauki matakin ne domin ta gyara bangaren sufurin jiragen saman kasar

Gwamnatin Najeriya ta ce ta karbe ikon kamfanin jiragen sama na Arik wanda ke fama da bashi mai dumbin yawa da ke neman durkusar da kamfanin.

An kwashe tsawon lokaci kamfanin Arik, wanda ke daukar nauyin kashi 55 cikin 100 na matafiya a kasar, yana fama da kalubale da dama.

Kamfanin yana ta fuskantar tangarda sakamakon rashin kyakkyawan shugabanci da matsaloli wajen gudanar da ayyukansa da rashin biyan ma'aikatansa albashi da kuma dumbin bashi da ake bin sa.

Wadannan matsaloli ne suka sa hukumomin kasar suka shiga tsakani domin shawo kan al'amarin saboda kar kamfanin ya rushe.

Matakin dai na nufin gwamnati za ta yi garanbawul a ma'aikatar sufurin jiragen saman kasar.

Yin haka kuma zai sa Arik wanda shi ne kamfanin jirgin sama mafi girma a kasar, ya ci gaba da aikace-aikacensa ba tare da samun tsaiko da kuma korar ma'aikatansa ba.

Za a kuma kare wadanda suka zuba jari tare kuma da tabbatar da cewa an warware matsalolin da bangaren sufurin jiragen saman kasar ke fuskanta.

Kaftin Roy Ukpebo Ilegbodu, wanda kwararre ne a harkar sufurin jiragen sama, shi ne zai jagoranci kamfanin.

Dama dai gwamnatin Najeriya ta sha tsoma baki cikin takaddamar da aka yi ta samu tsakanin kamfanin ARIK da kuma kungiyoyin ma'aikatan sufurin jiragen sama kan bashin naira biliyan 12 da kungiyoyin suka ce suna binsa.