Motocin gwamnatin Ghana sun yi batan dabo

shugaba Akufo-addo na Ghana

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shugaba Akufo-Addo ya sha alwashi kawar da cin hanci da almubazzaranci

Gwamnatin Ghana na kokarin gano motocinta sama da 200 da suka bata daga cikin tarin motocin ofishin shugaban kasa a cewar mai magana da yawun shugaba Nana Akufo-Addo.

Eugen Arhin ya ce wani bincike da aka yi bayan Mista Akufo-Addo ya karbi mulkin kasar a watan da ya gabata, ya gano cewa motocin sun bata.

Ya kara da cewa jami'a sun gano wadannan motocin ne kawai:

* Motoci kirar Toyota Land Cruiser guda 74 daga cikin 196

* Motoci kirar Toyota Land Cruiser Prado guda 20 daga cikin 73

* Motoci kirar Mercedes guda 20 daga cikin 24

* Motoci kirar Toyota guda 2 daga cikin 28

* Motoci kirar BMW guda 2 daga cikin guda 6

Sai dai tsohon ministan yada labarai Omane Boamah ya ce zargi ne kawai kuma wata hanya ce da sabuwar gwamnatin take so ta bi domin sayan sabbin motoci.

Mista Akufo-Addo ne ya kayar da John Mahama a zaben shugaban kasar da aka yi watan Disamban da ya gabata.