Gwamnati ta ji kokenmu - NLC

'Yan kungiyar NLC
Bayanan hoto,

Kungiyoyi da dama sun yi zanga-zanga domin nuna damuwarsu a kan matsin tattalin arzikin da ke kasar ke fama da shi

Shugabannin kungiyar sun shiga fadar shugaban kasar domin tattaunawa kan yadda za'a cimma matsaya kan bukatunsu.

Bayan shugabanin 'yan kwadagon sun gana da mukaddashin shugaban Najeriyar farfesa Yemi Osinbajo, sun bayyana wa mabiyansu cewar gwamnati ta ce ta ji kukansu.

Daga nan suka garzaya majallisar wakilan kasar inda suka gabatar da takardar kokensu ga Bukola Saraki, shugaban majalisar dattawan,

Mista Bukola ya ce gwamnati za ta dauki matakin rage radadin matsin tattalin arzikin da 'yan kasar ke ciki.

A ranar Laraba ne dai majalisar zartarwan Najeriyar ta bayyana matakan da za ta dauka domin rage tsadar abinci da 'yan kasar ke fama da shi.