Tafiya mai hadari don mu'amalar yau da gobe
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Tafiya mai hadari don mu'amalar yau da gobe

Kuna ganin zirga-zirgarku ta yau da kullum na da gajiyarwa?

Ba za ku gane kuna cikin ni'ima ba sai kun ga irin wahalar da mutanen kauyen Atuler da ke yankin Sinchua a kasar China ke sha, wajen saukowa daga kauyensu da ke saman wani tsauni mai nisan mita 800, don yin mu'amalarsu ta yau da kullum, kamar zuwa makaranta da asibiti da kasuwa da sauran hidimomi.