Chibok: Rayuwa ta sauya mana, mu na cikin walwala

Wasu daga cikin iyayen 'yan matan Chibok
Bayanan hoto,

Wasu daga cikin iyayen 'yan matan Chibok sun shaidawa BBC cewa ba su fidda rai gwamnati za ta kubutar da sauran 'ya'yan na su ba

A Najeriya harkokin yau da kullum sun kara kankama a garin Chibok na jihar Borno arewa maso gabashin kasar, bayan da hare-haren Boko Haram suka daidaita.

Yanzu haka matan garin da akasari sana'arsu noma ne, sun ce a shirye suke su sake komawa tsohuwar sana'ar ta su.

Da dama na fatan ganin sun fadada zuwa harkokin Kasuwanci don taimaka wa kansu da kuma 'yayansu su samu ilmi.

Yawancin matan da wata tawagar BBC ta zanta da su a lokacin ziyarar gani da ido da suka kai, sun bayyana yadda harkokin rayuwa ke tafiya yanzu a garin.

Sun shaidawa BBC irin bakar wahalar da suka sha a baya, a lokacin da 'yan Boko Haram suke yawan kai hare-hare a cikin garin na Chibok da kauyuka.

Yawancinsu sun fi rayuwa ne a dazuka na kwanaki, babu ruwan sha bare abinci har sai 'yan Boko Haram din sun fice daga garin.

'Yan Boko Haram sun yi musu illa ta hanyar sace musu kayan amfanin gonar da suka shuka, da shanunsu da sauran kayan bukatu na yau da kullum.

Cikin matan da BBC ta yi hira da su, akwai Malama Fala Aliyu, da kuma Fati Isa, sun ce a yanzu burinsu shi ne su kara fadada noman da suke yi na Gyada, da Gurjiya da sauran su.

Su na kuma fatan sauran 'yan matan sakandaren Chibok da har yanzu ke hannun 'yan Boko Haram, gwamnatin Najeriya za ta kubutar da su kamar yadda aka yi nasarar kubutar da wasu daga ciki.