Asibitin China ya shafa wa mutane biyar HIV

A shekarun baya-bayan nan an dage wajen wayar da kai kan cutar Aids a China
Wani asibiti a kasar China ya dauki alhakin cewa ya yi sanadin kamuwar mutum biyar da cutar HIV bisa kuskure, sakamakon yi musu amfani da kayan aikin da aka yi wa masu cutar amfani da su.
Jami'ai sun ce wani ma'aikacin asibitin ne ya yi amfani da wata roba da ake sanyawa marasa lafiya a hanci don basu abinci, wadda an riga an yi amfani da ita ga wani mai dauke da cutar Aids, ya sa wa wasu majinyatan da ba sa dauke da cutar.
Hukumomi a yankin sun kira wannan al'amari da cewa, "Babban sakaci ne na kaucewa ka'idar aiki."
Hukumar lafiya ta yankin ta ce tuni aka kori mutane biyar daga aiki sakamakon hakan.
Jami'an lafiya sun ce an sanar da su halin da ake ciki ne a aranar 26 ga watan Janairun 2017.
Amma a wata sanarwa da hukumomin suka fitar ba a bayyana ko akwai wasu karin marasa lafiyar da lamarin ya shafa ba.
Sanarwar ta ce za a bai wa wadannan mutane magani kyauta kuma za a biya su diyya.
Rashin ingantaccen tsarin lafiya ya taimaka sosai wajen yaduwar cutar Aids a China shekaru 20 da suka gabata, kuma labarin abin da ya faru a wannan asibiti ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a tsakanin masu amfani da kafafen sada zumunta na zamani.
Wani mutum ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa, "Idan har babban asibitin yanki na gwamnati ba zai dinga kula wajen bin tsari ba, ina za mu kama kenan a matsayin madogara mu 'yan kasa?"
"Wannan lamari wanda muka sani kenan, ina kuma ga wadannan ke faruwa ba mu sani? Lallai ba za a rasa irin haka da ya faru da yawa ba," abin da wani ya rubuta kenan shi ma a nasa shafin.
An samu karuwar masu cutar Aids sosai bayan a China bayan wata badakala da ta faru a yankin Henan a shekarun 1990, a lokacin da manoman da ke sayar da jininsu suka dinga daukar cutar saboda rashin ingantaccen tsari na kula.