An dambata a majalisar Afirka ta Kudu

South Africa
Bayanan hoto,

'Yan jam'iyyar EFF sun yi ta yi wa ZUma ihun sai ya yi murabus

An dambata sosai a majalisar dokokin Afirka ta Kudu yayin da 'yan majalisa na jam'iyyun adawa suka yi kokarin katse jawabin da shugaba Zuma yake yi kan halin da kasa ke ciki.

'Yan jam'iyyar Economic Freedom Fighters (EFF), masu tsattsauran ra'ayi wadanda duk suka yi shigar jan kaya, sun yi ta ba-ta-kashi da jami'an tsaron da suka fitar da su daga zauren majalisar.

Sau biyu shugaba Zuma yana mikewa tsaye don ya gabatar da jawabi amma sai ya koma ya zauna saboda ihun da 'yan jam'iyyar adawar ke masa.

A wajen zauren kuwa, 'yan sanda sun yi ta harbin bindiga don tarwatsa 'yan adawa da masu goyon bayan gwamnati.

An sha zargin Mista Zuma da cin hanci ana kuma sukarsa kan yadda ya jawo tabarbarewar tattalin arzikin kasar.

A baya duk lokacin da zai gabatar da jawabi, sai 'yan majalisar jam'iyyar adawa sun bukaci ya yi murabus.

Da shigar Mista Zuma majalisar a ranar Alhamis sai 'yan majalisar EFF suka fara ihun kiransa da 'Barawo', ciki har da babban jagoransu Julius Malema.

Su kuwa takwarorinsu na jam'iyyar da ke mulki sai suka dinga mayar musu da martani da ihun kiran sunan jam'iyyarsu "ANC, ANC."

Bayanan hoto,

'Yan sanda sun yi ta faman tabbatar da doka da oda

Sai dai duk da iface-ifacen da ake yi Kakakin majalisar Baleka Mbete, ta yi ta kokarin ci gaba da jawabin gabatarwa, amma ana katse ta.

Mista Malema ya kira shugaba Zuma da, "Mai taurin kai da ba zai taba sauyawa ba".

Ya kuma cewa Kakakin majalisar, "Bata da hakuri, mai son kan tsiya."

Ms Mbete ta cewa 'yan majalisar, "Mun yi hakuri da ku, mun yi ta baku dama ku bayyana ra'ayinku, amma abin naku yana neman wuce gona da iri."

A karshe dai sai da aka kira jami'an tsaro cikin zauren majalisar suka fitar da 'yan jam'iyyar EFF da karfin tuwo.

A yayin da su kuma 'yan jam'iyyar Democratic Alliance suka fice daga zauren suna cewa Mista Zuma bai cancanci zama shugaban kasa ba.