Fadada matsugunan Yahudawa bai dace ba — Trump

Israel
Image caption Isra'ila ta sha ginawa Yahudawa gidaje a matsugunan Falasdinawa

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce dokar fadada matsugunan Yahudawa ta Isra'ila ba alheri ba ce ga shirin zaman lafiya tsakaninsu da Falasdinu .

A hirar da ya yi da wata jaridar Isra'ila, Trump ya ce yana son Isra'ila da Falasdinu su yi amfani da hankalinsu, kuma ya ce ya yi amanna za a iya cimma matsaya kan takaddamar da suke yi.

Kafin a ranstar da shi shugaban kasar Amurka, Mista Trump ya nuna alamun cewa ba ya adawa da shirin gina matsugunan Yahaudawa kuma banagren masu tsatsauran ra'ayin mazan jiya na Isra'ila sun yi maraba da nasarar da ya yi a zaben shugaban kasa.

Netanyahu: Za mu gina wa yahudawa gidaje 6,000

Sai dai bayaninsa na baya-baya nan ya sake jaddada sanarwar da fadar White House ta fitar kan cewa, matsugunan Yahudawa da za a fadada ba alheri ba ne.

A farkon watan nan ne Firai ministan Isra'ila Benyamin Netanyahu ya yi alkawarin gwamnatinsa za ta bada izinin sake gina wasu matsugunan a yankin Palasdinawa bayan an dakatar da ginin yankin Amona.

Labarai masu alaka