New Zealand ta ceto manyan kifaye 100

Manyan kifaye da suka makale a bakin tekun New Zealand

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Wannan ne karo mafi muni da kasar ta fuskanta na makalewar manyan kifaye

Masu aikin sa kai a kasar New Zealand na kokarin ceto rayuwar kifaye guda 400 mafi girma a dauniya da suka tsira da rayukansu daga bakin tekun kasar.

Kusan manyan kifaye 300 ne suka rasa rayukansu a gabar tekun Farewell Spit da ke kusa da tsibirin Kudancin kasar, al'amari mafi muni da kasar ta taba fuskanta.

Tun a safiyar ranar Juma'a ne daruruwan 'yan garin da wasu jami'an kare dabbobi da muhalli ke ta kokarin ceto kifayen da suka rayu.

Masana kimiyya sun ce ba su san dalilin da ya sa manyan kifayen ke son fitowa su shanya kansu a bakin teku ba.

Amma wasu lokutan hakan kan faru saboda wasu daga cikinsu sun tsufa wasu kuma basu da lafiya, ko sun jikkata ko kuma sun yi batan hanya musamman idan igiyar tekun bata da karfi sosai.

A wasu lokutan idan babban kifi daya ya shanya kansa a bakin teku, ya kan aike da alamar cewa yana cikin wani halin kunci ga sauran manyan kifayen wadanda su ma suke makalewa saboda hawa da sauka na igiyar ruwan tekun.

Manyan kifaye na yunkurin kashe kansu idan suka makale?

Asalin hoton, REUTERS

Bayanan hoto,

Masu aikin sa kai na kokarin mayar da kifayen cikin teku

Jami'an da ke kula da dabobbi da muhalli sun ce sun samu rahotanni da ke cewa akwai yiwuwar wasu manyan kifayen sun makale a bakin teku a daren ranar Alhamis.

Jaridar New Zealand Herald ta rawaito cewa ba a fara aikin ceto ba har sai safiyar Juma'a saboda akwai hadari a tattare da aikin ceto cikin dare.

Wata kungiya Project Jonah, da ke aikin ceto a kasar New Zealand wadda ke gaba wajen ceto rayukan manyan kifayen, ta ce kifaye 416 ne suka makale.

Kungiyar ta ce 'yan gari da masu aikin lafiya sun kebe kifayen kuma suna zuba musu ruwa domin su ji sanyi su kuma kasance cikin kwanciyar hankali.

Ana Wiles daya daga cikin masu aikin ceton ta ce, "Mun yi kokari mun mayar da wasu daga cikinsu cikin teku kuma da yawa sun mutu a bakin tekun, abin da tausayi sosai."

Daya daga cikin abu mafi kyau shi ne, "Mun yi kokari mun mayar da akasarinsu kuma suna da jarirai da suka biyo su inji Ms Wiles.

New Zealand ce kasar da ke da manyan kifayen da ke makalewa a bakin teku mafi yawa a duniya, "ku san manyan kifaye na Dolphins da kuma Whales 300 ne ke makalewa a bakin tekun kasar a duk shekara," a cewar kungiyar.