Trump ya amince da kasancewar Taiwan wani bangare na China

Shugaba Donald Trump da shugaba Xi Jinping Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tattaunawar da shugabannin biyu su ka yi a wayar tarho ita ce ta farko tun bayan da shugaba Trump ya karbi mulkin Amurka

Shugaba Donald Trump ya janye barazanar da ya yi na yin fatali da manufar Amurka ta gomman shekaru ta China kasa daya.

A wata hira da shugaban Amurkan ya yi da shugaban China, Xi Jinping, Trump ya yi alkwarin ci gaba da manufar wadda za ta tabbatar da zaman lafiya tsakanin China da Taiwan kuma ta taimaka wajen gina dagantaka da Amurka na kusan shekara arbain.

A yammacin ranar Alhamis ne Shugabannin biyu suka yi wata hira wadda fadar White House ta bayyana da cewa mai tsawo ce kuma wacce za ta haifar da kyakyawar dangantaka.

A baya dai Donald Trump ya ambato yiwuwar fatali da manufar kin amincewa da Taiwan a matsayin kasa mai cin gashin kanta a hukumance.

Ya kuma ambato cewar za'a iya yarjejeniya kan hakan a harakar cinikayya da China.

A wata sanarwa, fadar White House ta ce Shugaba Trump ya martaba rokon da shugaban China ya yi ne wanda ya nemi ya mutunta manufar China daya.

China ta yi maraba da tabbacin da Donald Trump ya bayar na mutunta manufar China daya wadda wani ginshiki ne a dangantakar da ke tsakanin Amurka da China na kusan shekara arba'in.

Wani mai magana da yawun ma'aikatar kasashen wajen China, Lu Kan, ya yi maraba da sauya ra'ayi da shugaban Amurkar ya yi.

Amma kasar Taiwan ta ce Amurka ce babbar kawar da ta ke da ita a duniya.

Wani mai magana da yawun fadar shugabar Taiwan din, Alex Huang, ya ce, muhimmin muradin Taiwan shi ne wanzar da zaman lafiya da damokuradiyya da kuma cigaba da taka rawa a fagen duniya.

Labarai masu alaka