Wenger na dab da barin Arsenal - Wright

Arsene Wenger
Bayanan hoto,

Ian Wright ya ce alamu sun nuna Wenger ya fara gajiyawa

Tsohon dan wasan Arsenal Ian Wright, ya ce kocin kungiyar Arsene Wenger, na dab da barin kulob din.

Wenger ya kasance kocin Arsenal tun watan Oktoban 1996 inda ya lashe gasar Premier sau uku - ta baya-bayan nan a 2014.

Kwantiragin kocin mai shekara 67 za ta kare a karshen kakar wasanni ta bana.

Ian Wright ya shaida wa BBC cewa: "Na fahimci cewa lokacinsa ya zo karshe. Akwai alamar gajiya wa a tare da shi.

"Ina ganin a karshen kakar bana zai kama gabansa."

Fatan Arsenal na lashe gasar ta bana ya gamu da cikas bayan da Chelsea ta casa ta da ci 3-1, abin da ya mayar da ita mataki na hudu a kan tebur.

Wright ya ce ya yi magana da Wenger a ranar Alhamis da daddare.

"Alal hakika ya fada min cewa lokacinsa ya taho. Ban taba jinsa ya fadi hakan ba a baya," a cewar tsohon dan kwallon.

Ya kara da cewa 'yan wasansa sun zuba masa kada a ido.

Kawo yanzu babu wani martani daga Wenger, wanda ke fuskantar matsin lamba a baya-bayan nan, ko kuma daga Arsenal.