Hoton ma'aurata masu cutar Cancer ya ja hankalin jama'a

Hoton Julie da Mike Bannet a gadon asibiti
Bayanan hoto,

Ma'auratan sun rike hannun juna, gabannin mutuwarsu wanda 'ya'yansu suka ce sallama suke yi da juna

'Ya'yan wasu marasa lafiya da ke fama da cutar Kansa ko Sankara, sun wallafa hoton iyayensu gabannin mutuwarsu, a shafukan sada zumunta.

Hoton ya nuna Mike Bennet mai shekaru 57, da mai dakinsa Julie 'yar shekara 50, su na rike da hannun juna a lokacin da suke cikin mawuyacin hali a asibitin St John's da ke Birtaniya, inda suke karbar magani.

Kwanakin kadan ne tsakanin mutuwar ma'auratan da suka dade su na fama da jinya, inda Mr Bennet ya fara rasuwa sakamakon Kansar kwakwalwa da yake fama da ita.

Tuni 'yan uwa da abokan arziki suka kafa wata gidauniya, da za su tarawa 'ya'yan mamatan Oliver mai shekara 13, da Hannah mai shekara 18, da kuma Luke dan shekaru 21.

Kuma cikin kasa da kwana guda da kafa gidauniyar, har an samu dubban daloli daga mutane daban-daban.

Wata aminiyar Misis Julie, Sue Wright, ta shaidawa manema labarai cewa sa'o'i kadan gabannin mutuwarta, ta shaida mata ta kwantar da hankalinta jama'a za su tara kudin da za a tallafi rayuwar 'ya'yan ta ko bayan ta rasu.

''Sai ta dago idonta, ta yi min murmushi'', inji Wright.

A watan Mayun shekarar da ta gabata ne, aka tabbatarwa misis Julie ta kamu da cutar Kansa a hantarta, daga baya kodarta ta harbu, sai kuma ta mamaye cikinta baki daya.

Ya yin da mijin na ta, ya shafe shekaru 4 ya na fama da Kansar kwakwalwa, kuma maidakinsa ce ke jinyarsa tun lokacin da ya fara rashin lafiya.

A bara ne ita ma cutar ta bayyana a gare ta, likitoci a asibitin St John's suka hada su jinya a daki guda.